Baya ga matsalar tsaro wata matsalar da a yanzu ke damun talaka a Najeriya itace ta batun abincin, wanda masana ke gargadin cewa dole hukumomi a Najeriya su tashi tsaye wajen bunkasa harkar noma.
Kuma don amsa wannan kira, gwamnatin jahar Adamawa ta raba taraktocin noma 105, don taimakawa manoman dake kananan hukumomin Jahar don bunkasa harkar noma da rage radadin matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita.
Da yake kaddamar da raba taraktocin 105, gwamnan jahar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, yace manufar shirin shine farfado da harkar noma a jahar kamar yadda yayi alkawari yayin zawarcin kuri’un jama’ar jahar wanda akasarinsu manoma ne.
An dai raba taraktocin ne ga shugabanin kananan hukumomin jahar 21, inda shugaban kungiyar shugabanin kananan hukumomi ta Najeriya, ALGON, reshen jahar wato Barista Aliyu Wakili Boya ya nuna godiyarsu game da wannan taimakon.
A jawabinsa Lamidon Adamawa Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa, ya yaba game da matakan da gwamnatin ke dauka a yanzu wajen inganta harkar noma.
To sai dai kuma raba taraktocin noman dai na zuwa ne yayin da kungiyoyin manoma a jahar ke zargin ana nuna musu shakulatin bangaro ta bangaren tallafi.