Biyon bayan fashewar bam din an garzaya da gawarwakin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka sami jikkata zuwa Asibitin garin Michika.
A cewar wani daya tsallake rijiya da baya, yace da missalin karfen goma da minti biyar ne bam na farko ya fashe ne a kasuwar ‘yan Buhu inda yake sayar da kayyayakin gona, na biyun kuwa ya fashe a layin ‘yan Daddawa, wanda yanzu haka sauran ‘yan kasuwar sun nade kayansu tun tafi gida.
Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga hukumomin tsaron jahar Adamawa tukunna.
Shima dan Majalisar Wakilai dake wakiltar mazabar Madagali da Michika a Majalisar Tarayya Adamu Kamale, ya tabbatar da faruwar afkuwar lamarin amma yace ya zuwa lokacin da yake magana da wakilin Muryar Amurka, basu da masaniyar ko mutane nawa ne abin ya shafa.
Garin Madagali dake makwabtaka da jahar Borno, itace karamar hukuma ta karshe da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram, wanda kawo yanzu harkoki suka fara farfadowa a yankin inda har aka fara cin Kasuwa.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.