A taron ganawa da manema labarai da yayi a ofishinsa babban akanta janar na jihar Alhaji Garba Aliyu Maigamo yace gwamnan jihar ya bada umurnin a fara biyan ma'aikatan gwamnati albashinsu.
Inji Alhaji Maigamo gwamnan jihar yace alkawarin da ya dauka na biyan ma'aikata to a yi maza a cika. Ma'aikatan na bin bashin albashin watanni biyu kana 'yan fansho suna bin na wata daya.
Yayi bayanin abun da ya kawo tsaiko. Na farko Alhaji Maigamo yace sun samu matsala da babban bankin kasar. Wannan matsalar an warwareta.
Saidai kuma da aka tambayeshi yaushe za'a soma biyan ma'aikatan sai akantan jihar yace kudin da za'a turo masu dole sai an canzasu daga dala zuwa Nera. Yace akwai matakai da yawa da zasu dauka tun daga akanta janar na kasa zuwa fadar shugaban kasa.
Ma'aikatan da masu karban kudin fansho sun nuna shakku. Wani yace idan zasu biya sun gode amma kuma idan lamarin ya zama yaudara ba zasu ji dadi ba saboda gwamnan ya sha yi masu alkawari amma baya cikawa. Kwanaki ishirin da suka wuce yayi masu alkawarin biyansu cikin sati daya amma bai cika ba.
Wani yace gwamna da kansa yayi alkawari bai cika ba balantana dan aikansa akanta janar, sai dai addu'a kawai,inji mutumin.
Kawo yanzu dai ma'aikata da masu fansho babu wanda aka biya. Mutane na cewa gwamnati ke fada ta kuma karyata kanta. Saboda haka abun da shi akanta janar ya fada masu sai sun gani a kasa zasu yadda.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.