Al’umomin garuruwa 98 wadanda ke zaune a zagayen madatsar ruwan Zungeru sun garzaya kotun ne domin ganin an dakatar da aikin samar da tashar wutar lantarki a madatsar ruwan, wadda tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta kaddamar.
A cewar al’umomin har yanzu an kasa biyan diyyar gonaki da gidajensu da aka karbe sakamako gina madatsar ruwan, sun kuma ce wadanda suka sami kudadensu a shekarar da ta gabata an biya su N10,000.00 zuwa N15,000.00 a matsayin diyyar gonaki da kuma gidajensu.
Lauyan dake kare al’umomin yankin Chief Joshua Ajayi, yace an kwacewa mutanen gonaki da gidaje ba tare da nemar musu wani matsugunnin ba, sabanin alkawarin da akayi musu. Hakan yasa suke neman da a dakatar da aikin madatsar har sai an kammala biyansu hakkokinsu.
Sai dai kuma shi lauyan dake kare wadanda ake kara yace ba zai yi magana da ‘yan jarida ba. Tun a makon jiya gwamnatin jahar Neja ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda lamarin yake bisa la’akari da yawan korafe korafen.
Yanzu haka dai Alkaliyar kotun gwamnatin tarayya dake zama a Minna, mai Shari’a Elizabeth Bagoro, ta saka ranar 12 ga watan Janairun shekara ta 2017, domin ci gaba da sauraron karan.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.