A lokacin yakin neman zabensa, Trump ya yi alkawarin soke shirin na sassaucin inshorar asibiti, wanda ake kira Obamacare, amma tun lokacin ya nuna cewa akwai wasu sassan shirin da yake gani ya kamata su ci gaba da aiki.
Jiya litinin Trump ya gana da wani wanda ta yiwu ya zama sakataren harkokin wajen Amurka, wanda kuma ta yiwu ya tado da wasu Zafafan tambayoyi daga majalissar dokokin Amurka—wato tsohon shugaban hukumar leken asirin CIA, janaral mai ritaya, David Petraeus. Kafin ya shugabanci hukumar ta CIA, Petraeus ya taba zama babban kwamandan sojojin Amurka a Iraki ya kuma shugabanci rundunar tsaron NATO a Afghanistan.
Amma akan dole ya yi murabus daga hukumar ta CIA bisa wani abun kunya da ya faru a shekarar 2012, bayan bullar wasu bayannan sirri zuwa ga marubuciyyar tarihinsa, wadda ya nema.