A wani salon yakin neman zabe da ake ganin irin na Amurka ne, masu neman takara Francois Fillon mai shekaru 62 da kuma Alain Juppe mai shekaeru 71, wadanda dukkaninsu sun rike mukamin Firai minista, sun kasance ‘yan takara na gaba-gaba a zaben na fidda gwani.
Sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa, mai tsatsauran ra’ayin mazan jiya, Fillon, wanda ya yi alkawarin tunkarar matsalar ‘yan ta’adda, yana gaban Alain Juppe mai matsakaicin ra’ayi.
Wata ‘yar takara da ake sa mata ido a wannan zabe ita ce Marine Le Pen, wacce kalamanta na nuna kyamar baki da Musulmi ya ke jan hankulan masu zabe.
Ana sa ran a cikin makwannin da ke tafe, shugaba mai mulki, Francois Hollande ko zai bayyana aniyarsa ta tsaya wa takara a karo na biyu.