Babbar sufeton ‘yansandan birnin Columbus, Kim Jacobs tace suna kallon wannan farmaki a matsayin harin ta’addanci.
Hukumomin jami’ar ta Ohio sun bada sunan wanda ya kai harin da cewa ana kiran shi Abdul Razak Ali Artan, wanda ashe ma dalibin makarantar da ya kaiwa hari ne.
Mazauna garin dai sun gayawa sashen Somaliyanci na VOA cewa matashi, mai kamar shekaru 20, dan asalin Somalia ne.
Ta wani gefen irin wanan kuma...Baturen nan farar fata da ya kashe mutane bakaken fata guda 9 yayinda suke cikin wata coci a birnin Charleston dake jihar Carolina ta Kudu, ya samu iznin hukuma na ya wakilci kansa a matsayin lauyan kansa a shara’a da ake mishi na kisan kawunan da yayi.
A jiya Litinin ne wani alkali ya baiwa Dylann Roof iznin ya shirya zama lauyan kansa a shara’ar da za’ayi mishi inda zai fuskanci zargin aikata lafukka 33 wadanda suka hada da wadanda, idan aka same shi da laifin aikata su, ana iya yanke mishi hukuncin kisa.
Kudurin wannan Baturen na ya wakillci kansa a matsayin lauyan kansa ya biyo ne bayan cacar bakin da aka share wattani ana yi da shi bayanda yayi tayin cewa ya yarda ya amsa laifukkan da ake zarginsa da aikatawa idan hukumomi sun yarda su yanke mishi hukuncin daurin rai da rai maimakon hukuncin kisa, abinda hukumomin suka ki yarda da hakan.