A wata sanarwa da aka fidda, ministan harkokin wajen Faransa Jean- Marc Ayrault ya ce fiye da kowanne lokaci, akwai bukatar a gaggauta kawo karshen rikicin da ake yi da kuma samun hanyar kai taimakon jinkai ga mazaunan birnin da aka yiwa kawanya.
MDD ta ce mutanen da yawansu ya kai 16,000 sun gudu daga gabashin birnin Aleppo a cikin ‘yan kwanakin nan biyo bayan farmakin da dakarun gwamnati suka kai.
A yau Talata kungiyar sa idanu kan kare hakkin bil Adama ta kasar Syria mai hedkwata a Britaniya, ta ce an kashe akalla fararen hula 10 sakamakon hari ta sama da aka kai a Bab al-Nairab, daya daga cikin garuruwan da har yanzu ke hannun dakarun ‘yan tawaye.
‘Yan raji da kafar yada labaran gwamnatin Siriyya sun fada jiya litinin cewa mayakan gwamnati sun sami nasarori akan mayakan ‘yan tawaye a gabashin birnin na Aleppo, abinda ke cikin dabarar raba bangaren dake hannun ‘yan tawaye kashi biyu.