A karon farko dai gwamnan na Kano ya furta wasu kalamai dangane da wannan batu wadanda ke kara haskaka tsamin dangantaka a tsakanin su.
Litinin din makon jiya ne dai tsohon gwamnan na Kano kuma Sanata a yanzu Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kai Kano, domin ziyarar ta’aziyya amma daga baya ta rikice ta koma tamkar gangamin siysa inda magoya baya dauke da makamai iri-iri, suka rinka kalamai marasa dadin ji ga gwamna mai ci a yanzu.
Baya ga furta bayanan musanya Buhari da Kwankwaso a shekara ta 2019, lamarin dai ya sanya shugabancin jam’iyyar APC na Kano bayyana damuwa ainin, tare da kafa kwamitin bincike domin daukar matakin ladabtarwa akan Sanata Kwankwaso, kamar yadda shugaban jam’iyyar na kano Umar Haruna Doguwa ya shaidawa namema labarai.
To amma daga bisani shugaban ya lashe amansa yana mai cewa tursasa masa akayi. Sai dai kwamitin zartarwa a Kano ya mayar da martani game da wannan lashe amai, yana mai cewa aikin kwamitin bincike da ladabtarwa akan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yana nan daram.
Yayin da wannan al’amura ke faruwa a cikin jam’iyyar APC ta Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ci gaba da sanya takunkumi a bakin sa har zuwa maraicen jiya Litinin, inda a gurin ran gadin duba aikin hanya a cikin birnin Kano ya ke cewa, a jihar Kano ba zasu yarda a yaki Muhammadu Buhari ba.
Domin karin bayani.