Kakakin rundunar sojin Najerita Kanar Sani Usman Kukasheka shi ya bayyana wannan tsarin daukan nauyin yaran da suka rasa iyayensu a yaki da Boko Haram.
Yace kowane soja da ya rasa ransa rundunar zata dauki nauyin 'ya'yansa uku ta renesu tun daga ilimin firamare har jamai'a.
Rundunar zata yi aiki ne da kamfanonin inshora wadanda zasu dinga biyan kudaden makarantun yaran. Kudin da za'a kashe akan kowane soja ya ta'allaka ne akan matasyin da ya kai a aikin soji kafin ya rasa ransa.
Banda wannan shirin na inshora hukumar fansho ta sojoji zata biya kowane iyalin sojan da ya rasu albashinsa na shekaru biyar a dunkule. Akwai kuma kudaden taimakawa da hidimomin jana'iza da sauran abubuwa da za'a ba kowane iyali.
Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa kwararre akan aikin soji yace wadannan abubuwan da yanzu za'a yi ma sojoji zai kara masu karfin gwiwa ya kara masu kaimi suka kara sadakar da kansu ga aikinsu. Na baya ma zasu san cewa koda wani abu ya faru dasu shugabanninnsu zasu kula da iyalansu.
Ga karin bayani.