Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Kama Wani Babban Barawon Shanu A Jihar Neja


Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara
Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara

Hukumomin jihar Neja sunce sun cafke wani mutum da aka dade ana nema daga jihohin Zamfara da Katsina, bisa zarginsa da zama daya daga cikin kwamandojin barayin Shanun da suka Addabi jama’a.

Babban daraktan dake kula da sha’anin tsaro a ofishin gwamnan jihar Neja, kanal Maikundi Mai Ritaya, yace mutumin da ake zargin mai suna Na Imam, gwamnatin jihar Zamfara ta dade tana nemansa ruwa a jallo, amma sai a wannan lokaci ne aka samu nasarar damke shi a jihar Neja.

A halin yanzu dai a kwai wasu Shanun satar da yawansu ya kai 500 da aka kama a karamar hukumar Shiroro, amma wasu Fulani da suka fito daga Katsina sunce sunga wasu daga cikin Shanun su da aka sace wanda ba a basu ba.

Gwamnatin jihar Neja dai ta daurawa Kanal Mai Kundi Mai Ritaya alhakin kula da Shanun satar da aka kama, ya kuma bayyana dalilin rashin bayar da Shanun da sauri. Inda yace yana yiwuwa a sami matsala idan akayi saurin bayar da Shanun ga masu shi, domin akan iya baiwa wani kayan wani.

A kwanakin da suka gabata ma rundunar yan Sandan jihar Neja, tace ta samu nasarar cafke wasu muggan barayin Shanun tare da Shanun sata, har ma da wasu muggan makamai kamar yadda kwamishinan yan Sandan jihar Abubakar Marafa, ya tabbatar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG