Shugaba Buhari dai yace yana son ya fuskanci matsalar Boko Haram, a Arewa maso Gabashin kasar inda yace idan yayi maganin ta, to zai mayar da hankali zuwa Kudu maso Kudu domin kawo karshen satar gurbataccen Man fetur da fashi da akeyi akan jiragen ruwa, da shigo da makamai don yin ta’addanci.
Kakakin fadar shugaban kasar Najeriya, Mallam Garba Shehu, yace wannan ziyara ci gaba ne akan ziyarar da yake kaiwa ga makwabtan Najeriya.
Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Dakta Aliyu Idi Hong, yace wannan ziyara na da muhimmanci ga tarayyar Najeriya. Shima hafsan sojan Najeriya mai murabus Aliko El-Rasheed Haroon, na kallon wannan ziyara ne ta fuskar tsaro.
Domin karin bayani.