Kungiyar Miyetti Allah dai ta zargi gwamnatin jihar Taraba ne da cewa tana yiwa yayanta diban karan mahaukaciya ta hanyar hana su zuwa Taraba, batun da suka ce ba zasu kyale ba.
Mataimakin shugaban kungiyar makiyayan a Najeriya, Alhaji Usaini Yusufu Boso, yace ba zasu amince da abida ke faruwa a jihar ba, inda yayi Allah wadai da lamarin kuma yace idan har ya gagara suna iya daukar sa har gaban shugaban kasa zasu kai maganar.
A martanin da gwamnan jihar Taraba ya mayar Darius Dickson Ishaku, ta bakin hadiminsa ta fuskar harkokin siyasa Alhaji Abubakar Bawa, ya kuwa musunta zargin da kungiyar makiyayan ke yi ne. inda yace shi a iya saninsa babu wani mutum da yace a kori kowa a jihar.
Kakakin rundunar yan Sandan jihar DSP Josep Kwaji, yayi bayanin cewa bashi da labarin cewa ana korar wasu daga jihar, domin hakan zai sabawa dokar kasa.
Domin karin bayani.