An yanke hukumcin kisa a kan wasu sojoji 12 dake cikin masu yakar 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya a saboda yin bore da kuma kokarin kashe babban kwamandansu. A cikin hukumcin da Birgediya-Janar Chukwuemeka Okonkwo ya karanta, kotun soja ta samu wadannan sojoji 12 da laifi, yayin da ta sallami wasu biyar da ta ce ba su da laifi. An daure wani na tsawon kwanaki 28 a kurkuku tare da aiki mai tsanani.
An Yanke Hukumcin Kisa Kan Sojojin Najeriya Saboda Bore, 17 ga Satumba, 2014
![Wasu sojoji masu gabatar da kara ke zaune a layin gaba, yayin da wasau sojojin da ake tuhuma da laifin kai hari kan kwamandansu suka bayyana gaban wata kotun soja a Abuja, 17 ga Satumba, 2014.](https://gdb.voanews.com/5dab15b1-7561-4afc-880b-06e577916660_cx0_cy6_cw0_w1024_q10_r1_s.jpg)
1
Wasu sojoji masu gabatar da kara ke zaune a layin gaba, yayin da wasau sojojin da ake tuhuma da laifin kai hari kan kwamandansu suka bayyana gaban wata kotun soja a Abuja, 17 ga Satumba, 2014.
![Wasu sojoji masu gabatar da kara ke zaune a layin gaba, yayin da wasau sojojin da ake tuhuma da laifin kai hari kan kwamandansu suka bayyana gaban wata kotun soja a Abuja, 17 ga Satumba, 2014.](https://gdb.voanews.com/82325741-036b-45df-8c4a-a3534efb0cba_cx0_cy7_cw0_w1024_q10_r1_s.jpg)
2
Wasu sojoji masu gabatar da kara ke zaune a layin gaba, yayin da wasau sojojin da ake tuhuma da laifin kai hari kan kwamandansu suka bayyana gaban wata kotun soja a Abuja, 17 ga Satumba, 2014.
![星期六在纽约参加全美声援纽约市前警官梁彼得活动的与会者高呼“是事故不是罪犯”,“还梁彼得公道”。(美国之音方冰拍摄 2016年2月20日) ](https://gdb.voanews.com/85946feb-2729-4e05-bd08-37fb4ecd0d6c_cx0_cy1_cw0_w1024_q10_r1_s.jpg)
3
星期六在纽约参加全美声援纽约市前警官梁彼得活动的与会者高呼“是事故不是罪犯”,“还梁彼得公道”。(美国之音方冰拍摄 2016年2月20日)
![An yanke ma sojojin Najeriya hukumcin kisa bisa tuhumar yin bore a bayan da suka harbi babban kwamandansu a Maiduguri a cikin wannan shekarar, 17 ga Satumba, 2014.](https://gdb.voanews.com/2536ef87-738e-45c8-bd55-384c174d91ce_cx0_cy1_cw0_w1024_q10_r1_s.jpg)
4
An yanke ma sojojin Najeriya hukumcin kisa bisa tuhumar yin bore a bayan da suka harbi babban kwamandansu a Maiduguri a cikin wannan shekarar, 17 ga Satumba, 2014.