Yanzu haka kudurin ya kai matakin karatu na biyu bayan da ya wuce matakin karatu na farko.
Sanata Omo Agege wanda ya canza sheka daga jam'iyyar Labor zuwa APC shi ya gabatar da kudirin.
Sanatan ya ce akwai fiye da Naira tiriliyon uku da aka jibge a bankunan Najeriya da masu su basa ma batunsu ko kuma rai ya yi halinsa.
Yace duk kudaden da suka shekara goma a ajiye a bankuna ba'a taba su ba tamkar babu mai su ne.
Kuma gwamnati za ta iya amfani da su wajen gyara hanyoyi da samar da wutar lantarki da dai sauransu.
A cewar Sanatan lokacin da masu kudin na zahiri suka bayyana za'a iya biyansu tare da kudin ruwa mai araha.
Sai dai ana shi tsokacin masanin tattalin arziki, Malam Kasimu Garba Kurfi, ya ce dokar tana da wuyar aiwatar wa ko da an samar da ita.
"Ko an yi irin wannan dokar kotu na iya warwareta domin kudin ba na gwamnati ba ne." In ji shi.
Malam Kurfi ya ce akwai kudaden da ba mantawa aka yi dasu ba inda ya kara da cewa sabani cikin iyali ka iya hana taba wasu ajiya a bankuna.
Yayi misali da abun dake faruwa da iyalan tsohon madugun 'yan tawayen Najeriya Odumegwu Ojukwu.
"Bayan ya rasu shekaru da dama har yanzu iyalansa na shari'a akan kaddarorinsa ba'a iya rabawa ba. Ke nan tun lokacin da ya rasu kudadensa dake bankuna ba'a tabasu ba kuma ba wai an manta dasu ba ne."
A ganin Kurfi 'yan Majalisa sun bar abin da ya kamata su yi ba su yi ba sun maida hankali akan kudaden mutane.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya da tsokacin da Malam Kasimu Kurfi ya yi:
Facebook Forum