Jami’an Canada sunce suna da niyyar mika wani hamshakin attajirin nan dan kasar Tunisia,surkin shugaban kasar da aka hambare Zine El-Abidine Ben Ali.Attajirin da ahaklin yanzu yake gudun hijira a kasar.
Gwamnatin rikon Tunisia ranar Laraba c eta bada sommacin aka kama Belhassen Trabelsi.Haka kuma gwamnatin ta bada wani sommacin domin kama tsohon shugaban kasar Ben Ali,wanda ya tsere daga kasar da sauran iayalansa.
Ana zargin Trabelsi da kuruciyar bera daga bitul malin kasar.Ya isa Montreal Canada ranar 20 ga watan nan.
Masu zanga zanga a Tunisia waanda suka tilastawa Mr. Ben Ali gudu daga kasar,sun kuma nuna fushinsu kan Mr.Ben Ali da wasu daga cikin danginsa.Masu zanga zanga sun wawushe wani ksaitaccen gidan Belhassan suka kuma kona shi,jim kadan bayan da shugaban kasar ya tsere daga kasar.
‘Yan kasar Tunisia suna kira dangin tsohon shugaban kasar “Dangi” lakabi da aka fi amfani da shi wajen kiran kungiyoyin barayin zaune, ko “Mafia”.Suna kallon Trabelsi a matsayin jagoran mafiyar Tunisia.
Tunisia ta bukaci Canada ta yi wa dukiyar da kadarorin Trabelsi daurin talata,ta soke visarsa yayinda take shirya takardun mika shi ga Tunisia.