"Babu shakka,gwamnatin Hosni Mubarak, wacce aka sani da cin hanci da rashawa, da kuma danne hakkin jama’a, tana dangantaka zanga zangar da addini domin ta tsorata hukumomin kasa da kasa. Amma haka ba gaskiya bace. Kungiyarmu mai sassaucin ra’ayi ne, da son zaman lafiya, amma abin takaici kasashen yammacin Duniya, musamman ma Amurka, tana tsoron masu kaunar addini. Hakika ba’a rasa masu matsanancin ra’ayi nan-da-can ba, duk da haka kungiyar mai sassaucin ra’ayi ne, inji Abdel Mounoum Abdel Futuh, shugaban kungiyar Muslim Brotherhood, a hira da ya yi da Muriyar Amurka."
Saurari: Turanci, Abdel Mounoum Abdel Futuh, shugaban kungiyar Muslim Brotherhood
Saurari: Arabiyya, Abdel Mounoum Abdel Futuh, shugaban kungiyar Muslim Brotherhood