Masu zanga zanga sun shiga titunan birnin Washington da kuma wasu biranen kasashen duniya domin nuna goyon bayansu ga gangamin rajin damokaradiya a kasar Misira. Jama’a sun yi jerin gwano zuwa ofishin jakadancin kasar Misira dake birnin Washington yau asabar. Daga baya kuma suka kama hanya zuwa fadar White House. An kuma yi irin wannan zanga zangar ruwan sanyi jiya a nan Washington. Shafin sadarwar duniyar gizo Standtogethernow.org ya yi kira da a yi zanga zangar nuna goyon bayan mutanen kasar Misira a wurare dabam dabam na kasashen Amurka da kuma Turai. An kuma yi zanga zanga a harabar ofishin jakadancin kasar Misira dake birnin Amman, Jordan yau asabar, ana kira ga shugaban kasa Hosni Mubarak ya yi murabus a kuma yi garambawul a kasashen larabawa gaba daya. Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya laburta cewa, dalibai a kasar Iran sun yi zanga zanga a harabar ofishin jakadancin Misira dake Tehran yau asabar.
Masu zanga zanga sun shiga titunan birnin Washington da kuma wasu biranen kasashen duniya domin nuna goyon bayansu ga gangamin rajin damokaradiya a kasar Misira