Jami’an gudanar da zaben raba gardama na kudancin Sudan sun ce sakamakon farko na zaben yana nuni da cewa akasarin wadanda suka kada kuri’a sun zabi ballewa daga arewaci a kuri’ar da aka kada farkon wannan watan. Adadin da aka buga a yanar gizon hukumar zaben ya nuna dukan kuri’un da aka kada a kudanci da kuma arewacin Sudan, inda kusan kashi casa'in da tara bisa dari na wadanda suka kada kuri’a suka zabi ballewa. Yau Lahadi aka sanar da sakamakon zaben karon farko a bainin jama’a a wani buki da aka yi a Juba babban birnin kudancin Sudan da ya sami halartar shugaban kudancin Salva Kiir. Ana kyautata zaton fidda cikakken sakamakon zaben ranar sha hudu ga watan gobe na Fabrairu.
Sakamakon farko na zaben raba gardama na nuni da cewa akasarin wadanda suka kada kuri'a sun zabi ballewa daga arewaci.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024