Fiyeda shugabannin kasashen Afirka 25 ne suka isa Addis Ababa,babban birnin Habasha,domin taron kolin kwanaki biyu da zai fi maida hankali kan matsalolin tsaro da siyasa.
Taron na shekara shekara da aka bude lahadi, zai kuma kunshi kananan tarurrukan kolin gameda Ivory Coast,Sudan,da kuma Somalia,haka kuma mahalarta taron zasu tattauna kan wasu kasashe da ake da damuwa da akansu, da suka hada da Nijar da Madagascar.
Shugaban majalisar gudanarwar Tarayyar Jean Ping, yace sabbin matsalolin siyasa da suka barke a Masar da Tunisia, basa cikin ajenda.Yace wadan nan fitinu sun kunno kai dab da fara taron kolin wadda da wuya ya gabatar dasu ga taron shugabannin kasashen nahiyar.
Jiya Asabar ce babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki-moon, ya isa Adis Ababa,kuma shine zai jagoranci zama da za’a yi kan Ivory Coast, da Sudan.
Taron koli kan Ivory-Coast,zai maida hankali wajen daukan sabbin matakan difilomasiyya domin warware cijewarda aka asamu kan rikicin siyasar kasar,bayan da shugaba mai ci Laurent Gbagbo, yaki ya mika mulki ga Alassane Ouattara,mutuminda Duniya duka ta amince shine ya lashe zaben kasar.
Lahadin nan ne ake sa ran kafa kwamiti mai wakilai biyar,da nufin warware rikicin siyasar kasar.