Dubun dubatan masu zanga zanga sun bijirewa dokar hana yawon dare da aka ayyana a birnin Alkahira da ta shiga kwana na uku, suna neman shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus bayan shafe shekaru talatin bisa karagar mulki. Jiragen saman yaki suna ta shawagi a kasa kasa yayinda dubban mutane suka taru a dandalin Tahrir Square na birnin Alkahira yau Lahadi domin yiwa sama da mutane dari da aka kashe addu’a. Babban Jagoran hamayya Mohammed ElBaradei tsohon shugaban hukumar makamashi ta duniya, ya shiga sahun masu zanga zangar yau Lahadi. Ya shaidawa tashoshin talabijin na CNN da kuma CBS cewa, mutanen kasar Masar da kuma kungiyoyin hamayya sun dora mashi alhakin tsaida yarjejeniyar kafa gwamnatin gamin gambiza. Ya kuma ce gwarjinin Amurka yana raguwa a ikirarinta na ganin an bin tafarkin damokaradiya yayinda take ci gaba da goyon bayan shugaban kasar Masar. Yace ya kamata Mr. Mubarak ya fice daga Misira “yau”.
Dubun dubatan masu zanga zanga sun bijirewa dokar hana yawon dare da aka ayyana a birnin Alkahira da ta shiga kwana na uku.