‘Yan sandan sun kara da cewa suna aiki kafada da kafada da sojoji da kuma sauran jami’an tsaro domin ganin an yi zaben ciki kwanciyar hankali.
Wannan batu ya taso ne a daidai lokcin da hukumomin kasar suka haramta yin amfani da mutum-mutumi gabanin zaben.
Hukumar zaben kasar ta ce ta lura akwai karuwar masu amfani da wannan tsari wajen yin kamfen dinsu, duk da cewa ta haramta yin hakan tun a shekarar 2010.
Kakakin ‘Yan sanda, Fred Enanga, ya ce sun kaddamar da wani aikin cire duk wani mutum-mutumi, domin a cewarsa hakan ka iya barzana ga tsaro a lokutan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da kuma na kananan hukumomi.