Kungiyar AQMI wadda take reshen Al-Qaida dage yankin Maghreb, sun dai sace Josephine Elio da mijinta Dakta Ken Elio, a garin Jibo ranar 15 ga watan Janairu ranar da ‘yan ta’adda suka kai hari kan fitatcen Otal din nan mai suna Splendid na birnin Ouagadougou. Wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 30.
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ne ya karbi wannan mata yar kimanin shekaru tamanin da hudu da haihuwa, lokacin da yake yada zango a garin Doso a karshen mako.
A cikin jawabin shugaban Nijar, yace tun a ranar da aka sace wadannan turawa, hukumomin Burkina Faso suka bukaci hadin kan mu domin samo hanyoyin karbo su, saboda haka ne suka dage domin ganin an samo su.
Josephine da mijin ta sun shafe shekaru a kalla arba’in suna aikin jin kai a Asibitin garin Jibo, domin taimakawa al’umomin kan iyakar Burkina Faso da Nijar da Mali, sabada haka ne ma shugaban Nijar yace ya kamata su gane cewa wadannan turawan kasar Australia, sun taimakawa kasashen uku ta hanyar inganta rayuwar masu karamin karfi.
Wata majiyar harkokin wajen kasar Burkina Faso ta tabbatar da cewa, an samu ceto mutanen ne daga ‘yan kungiyar ta AQMI batare da biyan kudaden fansa ba.