Wannan gargadin dai ya biyo bayan sakamakon rahoton da majilisar ta samu ne wanda ya bayyana cewa an kiyasta a kalla mutanen da yawan su ya kai mililan 2.8, wanda wannan yana nufin adadin kashi 23 kenan na mutanen kasar zasu fuskanci wannan iftilain tsakanin cikin watan Janairu da na Mayun wannan shekarar.
Rahoton yaci gaba da cewa yawancin wadannan mutanen da wannan lamari zai rutsa dasu ko suna zaune ne a yankin Unity Jonglei da kuma can samar yankin kogin Nilu, wannan adadin kuma yakai na kashi 57 ne na ‘yan rabbana ka wadata mu.
Majalisar Dinkin Duniya tace wani abin shakkun kuma shine ana hasashen wannan lamarin ya kara muni tsakanin watan Afirilu zuwa watan Juli, lokacin da abinci zaiyi kasa kwarai da gaske kana yunwa ta kara tsananta.