Kakakin gwamnatin Somalia, Abdissalam Ahmed Ato, ya gayawa Muryar Amurka cewa hotonan bidyon sun nuna yadda mutanen biyu suka mikawa mutumin na’urar computer a asirce.
Haka zalika hotunan sun nuna cewa lallai mutumin ne ya rasu bayan da aka samu fashewar.
A kwanakin baya, wani jami’in tattara bayanan sirrin kasar, ya gayawa Muryar Amurka cewa, ana tsare da wasu ma’aikatan filin tashin jiragen da na kamfanin jirgin Daallo domin a tuhume su.
A cikinsu har da wasu mutane biyu da ake ganin babu haufi su suka taimaki mutumin da ake zargi da haddasa fashewar.
Abdissalam ya kara da cewa masu bincike suna rike da mutane 20 ya zuwa yanzu, kuma cikinsu akwai wasu ma’aikatan gwamnati da wasu ‘yan kasuwa da suka taimakawa mutumin da ake zargin.