A ranar 21 ga wannan wata na Fabrairu ‘yan kasar za su garzaya zuwa rumfunan zabe domin zaben wanda su ke so.
Akalla ‘yan takara 15 ciki har da shugaba mai ci Muhammadu Isufu ne za su fafata wajen neman shugabancin kasar.
Ba a dai taba ganin yawan ‘yan takarar neman shugabancin ya kai haka ba sai a wannan shekara.
A karshen makon da ya gabata aka kaddamar da yakin neman zabe a kasar inda tuni ‘ya takara suka fara shiga sako-sakon kasar domin neman kuri'u.
A lokacin da ya fara yakin neman zabensa a makon da ya gabata, shugaba Isufu ya ce zai lashe zaben tun a zagaye na farko.
Sai dai ‘yan adawa sun ce wannan ikrarin shugaban duk barazana ce da kuma dabarar siyasa.
Sauarari bukatun da wasu daga cikin matan kasar suka bayyana su ke so a biya musu ga dan takarar da ya lashe zaben: