Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Wani Mutum Da Kashe Mahaifiyarsa Da Tabarya A Bauchi


Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad

An fara gudanar da bincike game da afkuwar lamarin sannan an gano tabarya da aka aikata laifin da ita domin gabatarwa a matsayin shaida.

Ana zargin wani matashi mai shekaru 20 da hallaka mahaifiyarsa da tabarya a jihar Bauchi.

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ce ta kama matashin, Safiyanu Dalhatu saboda zarginsa da lakadawa mahaifiyarsa mai shekaru 40, Salma Abdullahi, duka da tabarya har lahira.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar, Ahmad Wakili ya fitar, mambobin kwamitin 'yan sintirin yankin Abujan Kwata dake garin Bauchi ne suka kai rahoton afkuwar lamarin ga caji ofis din 'yan sanda a ranar 24 ga watan Fabrairun da ya gabata.

"Ana zargin Safiyanu Dalhatu da afkawa salma abdullahi da katuwar tabarya, abinda ya sabbaba mata karaya a dukkanin hannuwanta 2 da kuma raunuka a sauran sassan jikinta," a cewar Wakili.

An fara gudanar da bincike game da afkuwar lamarin sannan an gano tabarya da aka aikata laifin da ita domin gabatarwa a matsayin shaida.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG