Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin kwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maboyarsa dake Legas.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun ndlea, femi babafemi, ya fitar, kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa ne bayan shafe shekaru 17 yana buya domin fataucin miyagun kwayoyi na bilyoyin nairori a fadin duniya.
Ya kara da cewa shugaban NDLEA, Burgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a yau Litinin.
Shugaban NDLEA ya kuma bayyana yadda jami'an sashen ayyukan musamman na hukumar suka rika bin diddigin Ogbonnaya biyo bayan nemansa ruwa a jallo da hukumar 'yan sandan duniya INTERPOL ke yi da kuma bayanan sirrin da hukumar leken asirin Koriya ta Kudu ta samar a kansa.
Dandalin Mu Tattauna