Kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayyar kasar na daidaita kudin lantarki tsakanin kwastomominsu da ke kan tsarin biyan kudi na A, D da C.
A sanarwar bayan taron da ta fitar a jiya Lahadi bayan kamalan taron kwamitin zartarwarta na kasa a birnin Yola na jihar Adamawa, kungiyar kwadagon ta sha alwashin jagorantar zanga-zangar gamagari a fadin Najeriya matukar gwamnatin ta ci gaba da shirin nata.
A Alhamis din da ta gabata, ministan lantarki, Adebayo Adelabu, yace za a daga likkafar kwastomomin da ke kan kananan tsarin biyan kudin wuta zuwa tsarin A.
A sanarwar bayan taron data fitar mai dauke da sa hannun babban sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, kungiyar kwadagon ta yi watsi da tursasawa masu amfani da lantarki koma kan tsarin biyan kudin wuta na A.
Dandalin Mu Tattauna