Sabbin alkaluman kididdigar da kamfanin samar da lantarkin Najeriya (TCN) ya fitar sun nuna cewar yawan lantarkin da kasar ke samarwa ya haura zuwa megawatt 5, 713.60 a yau Talata.
Alkaluman baya bayan nan da TCN din ya fitar sun bayyana cewa matakin da kasar ta kai a bana shine mafi girma a cikin shekaru 4 da suka gabata.
A cewar TCN, an yi nasarar rarraba ilahirin megawatt 5, 713 na lantarkin da aka samar a yau Talata.
A ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata Najeriya ta samar da megawatt 5, 543 na lantarki.
"An samu kaiwa ga wannan sabon mizanin ne a yau Talata, 4 ga watan Maris din da muke ciki da misalin karfe 9 da rabi na safiya, inda lantarkin da muke sanarwa ya kai megawatt 5, 713.60, abinda ya zarta rimin da yayi a baya na megawatt 5,543.20 da aka gani a ranar 14 ga watan Febrairun daya gabata da megawatt 170.40," kamar yadda TCN ya bayyana.
Dandalin Mu Tattauna