Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mojisola Meranda ta yi murabus daga kan mukaminta.
Meranda, wacce ta sanar da da batun yin murabus din nata yayin zaman majalisar na yau Litinin, tace ya zama wajibi ta yi sadaukarwa ta kashin kai domin kare martabar majalisar.
Haka shima, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Legas, Mojeed Fatai, ya sauka daga kan kujerarsa.
Kakakin ta ajiye mukaminta ne bayan wata ganawa da Mudashiru Obasa, tsohon kakakin majalisar dake fama da wutar rikici da shugaban jam'iyyar APC na jihar Legas, Cornelius Ojelabi da antoni janar na jihar, Lawal Pedro.
An Sake Zabar Obasa A Matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas
An sake zabar Mudashiru Ajayi Obasa a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Legas kasa da watanni 2 da tsige shi.
Haka kuma an sake zabar wacce ta maye gurbin Obasa bayan tsige shi, Mojisola Lasbat Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar biyo bayan murabus din da ta yi daga kan kujerar kakakin majalisar.
Dandalin Mu Tattauna