Alkalin Alkalan jihar Lagos, mai Shari’a Olufumilayo Atilade, ta bayar da sanarwar yin afuwa ga ‘yan Fursunar bayan wata ziyara da ta kai gidan yari na Kiri-Kiri. Akasarin masu zaman jiran Shara’ar dai sun shafe fiye da shekaru 15 suna zaman jiran Shari’a, a inda laifukan da suka aikata ya kama daga manya da kanana. Kuma koda shari’ar za’ayi musu bai fi a basu hukuncin dauri ko tara ba, amma sai gashi sun shafe shekarun da suka wuce wanda doka ta tanadar musu.
Alkalin Alkalan wadda ta ja hankalin wadanda aka sakin da su kasance masu da’a da bin umarnin doka da oda, tace ta dauki wannan mataki ne a karkashin ikon da dokar kasa ta baiwa ofishinta, na sakin fursunoni bisa jin kai, da kuma rage cunkoso a gidajen Yarin kasar.
Haka kuma ta bukaci sauran masu fada aji a bangaren Shari’a da kuma gwamnati da suma su bayar da tasu gudunmawar wajen rage cunkoso a gidajen Yarin Najeriya.
Bincike dai ya nuna cewa gidan Yari na Kiri-Kiri da ke zama mafi girma a kasar wanda kuma aka rabashi gida biyu, wanda aka gina domin daukar Fursinoni kimanin 2700 yanzu haka akwai Fursunoni fiye da 4000, daga cikinsu kuma guda 3500 ne ke jiran shari’a, a yayinda 337 kawai aka yankewa hukunci.
Domin karin bayani.