Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar rajin kare hakin bil'Adam ta bukaci a hukumta wadanda suka kashe 'yan shiya a Kaduna


Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Kungiyar rajin kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta kira a gabatar da shari’a biyo bayan jawabin da jihar Kaduna ta fidda na cewa an binne gawarwakin ‘yan shi’ar da aka yiwa kisan gilla kusan guda 350 a cikin kabari daya.

Jami’an jihar Kaduna sun bayyanawa Kwamitin binciken lamarin a ranar Litinin din data gabata cewa, an binne mutanen ne biyo bayan hatsaniyar da mabiya Shi’ar da sojoji a garin Zaria cikin watan Disambar bara.

Shugaban reshen kungiyar Amnesty da ke Kaduna M. K. Ibrahim yace, “wannan sanarwa mai razanarwa game da bibbindige ‘yan shi’ar da tona kabarin da aka binne gawarwakinsu, shine matakin farko da ya kamata a yi domin gurfanar da duk wadanda ake zargi da aika-aiakar.

Shugaban Hukumar al’amuran addinai ta jihar Kaduna Muhammad Namadi Musa, ya fadawa Kwamitin cewa, an umarceshi da bin tawagar Kwamishinan ‘Yan Sandan Kaduna don zuwa Zari’a, inda yace yaga dimbin gawarwaki a kan titi da suka hada da mata da yara cikin bakaken kaya.

Ya kuma ce an kidaya gawa 156 a asibitin Jami’ar Ahmadu Bello aka kuma karbi wasu gawarwaki 191 daga asibitin barikin Soji na Zaria. Wani ma’aikacin lafiya a asibitin Jami’ar ta Zaria kansa yace sai da ya kidaya gawarwaki akalla 400, suma mazauna unguwar da aka yi rikicin sun ce gawarwakin da suka cika kan titin wajen na da yawa sosai.

Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai yace sun aikata abinda ya faru a Zaria ne bisa dokar da aikin Soja ya tanada. Su kuma ‘yan Shi’a sun musanta cewa sun kaiwa Hafsan Sojan hari kamar yadda ake fada.

A baya dai an zargi sojojin Najeriya da cin zarafin bil’adama akan ‘yan Boko Haram wanda sojin suka ce basu yi wani mugun abinda bai kamata ba.

Ga karin bayani.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG