Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An fara Tuhumar Matan da Ake Zargi da Kisan Kim Jong Nam


Kasar Malaysia ta fara tuhumar wasu mata biyu da laifin kisa a yau Laraba.

Wannan tuhumar dai na da nasaba da mutuwar Kim Jong Nam, dan uwan shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un.

Siti Aisyah mai shekaru 25 ‘yar Indonesia da kuma Doan Thi Huong mai shekaru 28 daga Vietnam suna karkashin kwararan matakan tsaro, a lokacin da suka bayyana a gaban kotu a birnin Kuala Lumpur.

Ba a nemi matan su roki afuwa a wannan shari’a ba, sai dai sun ce ba su da masaniya a wannan zargi da ake musu inda suka ce suna zaton suna cikin masu wasan barakwanci na gidan telbijin ne.

Dukkansu za su fuskanci hukuncin kisa idan har an tabbatar da laifin a kansu.

Ana zargin matan biyu da hotunan bidiyon jami’an tsaro suka nuno su, suna shafa wani abu a fuskar Kim Jong Nam a filin saukar jiragen sama a Kuala Lumpur a watan da ya gabata.

Kim Jong Nam ya kuma mutu bayan minti 20.

Masu shigar da kara suna son su yi shari’ar matan biyu tare kuma za su sake bayyana a gaban kotun a tsakiyar watan Afrilu.

Matan biyu sun kasance sanye da riguna masu sulke yayin da aka raka su daga kotun zuwa gidan yari bayan zaman shari’ar da aka yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG