Rahoton yaci gaba da cewa, yayinda kungiyoyi kamar al-Qaida, da Boko Haram da al-Shabab suke ci gaba da kai hare hare da nufin gurgunta harkokin kasashensu, ISIS ta ci gaba da zama babbar barazana a duk fadin duniya a bara, inda take da "dakaru masu yawa da karfi" a Syria da kuma Iraqi.
Rahoton ya ci gaba da cewa, koda shike karfin mayakan kungiyar ya ragu a wani lokaci a bara, duk da haka 'yan yakin sakan kungiyar sun lallaba suka kai jerin hare-hare a wasu wurare da suka hada da Faransa da kuma Turkiya.
Haka nan rahoton na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurkan ya ci gaba da cewa, ISIS ta yi karfi a Libya, kuma ta kafa rassa a a Afghsnisdtan, da Pakistan da kuma Najeriya.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurkan tana ayyana kungiyoyi daban daban har 60 a zaman kungiyoyin 'yan ta'adda a rahoton nata na shekara shekara, haka nan tana ambaton kasashe da take kallonsu a zaman wadanda suke hana ruwa gudu a fafaftawa da ake yi da ta'addanci.