Ministan harkokin wajen kasar Abdul-Malik al-Mekhlafi, ya kira shawarwarin da ake yi a Kuwait a zaman "bata lokaci." Yace 'yan tawayen sun dage tilas sai an yi daunin iko, maimakon su mutunta kudurin kwamitin sulhu na MDD wanda yace wannan batu ne da sassan biyu zasu yi shawara akai.
Ministan ya zargi 'yan tawayen na Houthi da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar, sannan suna amfani da shawarwarin a zaman wata dama ta sake yin damara.
Zuwa yanzu dai 'yan tawayen basu maida martani ba kan dakatar da wannan shawarwarin sulhun.
Kungiyar 'yan tawayen da take samun daurin gindi daga Iran ta kwace Sana'a babban birnin kasar a shekara ta 2014, mataki da ya tilastawa gwamnatin kasar da duniya ta amince da ita gudu zuwa kasar Saudiyya, kamin daga bisani ta dawo ta kafa cibiya a birnin Aden mai tashar jiragen ruwa.
Fadan da ake gwabzawa, tareda farmaki daga sama da kasar Saudiyya take kaiwa kan 'yan tawayen Houthi, ya janyo mummunar yanayin rayuwa ga al'umar kasar, har MDD tana cewa kashi 80 na farar hula dake Yemel suna bukatar agajin gaggawa na abinci da kuma kiwon lafiya.