Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Kurdawa Sun Tashi Kwato Birnin Raqqa daga ISIS


Mayakan Kurdawa
Mayakan Kurdawa

Kungiyar mayakan sakan kurdawa a Syria da ake kira Democratic Forces ko SDF a takaice, ta kaddamar da wani mataki na kwato wasu sassa dake arewacin birnin Raqqa, gari da kungiyar ISIS take dauka a zaman helkwatarta, da zummar 'yanto birnin baki daya.

Kungiyar mai kawance da Amurka ta bada wannan sanarwar ce ta bidiyo data saka a internet jiya Talata. "Muna kaddamar da wannan farmakin ne tareda taimakon runduar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci a a arewacin Raqqa," inji Rojda Felat, wata kwamandan mayakan kurdawa.

Wani babban kwamandan kungiyar ya gayawa Muryar Amurka cewa, dakarun dake karkashinsa sun tasamma birnin daga kusurwa uku,. Yace "tuni aka aike da tankunan yaki da wasu manyan makamai.

Kakakin rundunar taron dangin, karkashin jagroancin Amurka Kanar Steve Warren, yaki ta tabbatar da irin rawar da sojojin na taron dangi zasu yi a farmakin da SDF take shirin zata kai.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, a lokacinda yake ziyara a Uzbekistan yace, a shirye Moscow take ta hada kai da kurdawa da kuma runduar taron dangin da Amurka take yiwa jagoranci wajen 'yanto birnin na Raqqa. Amma, Amurka bata bada karfi kan batun zata yi aiki da Rasha a kokarin 'yanto birnin Raqqa ba.

XS
SM
MD
LG