Jerin bamabaman sun fashe ne a yakunan da gwamnatin kasar take da karfi a biranen Jableh da Tartus.
Kafin wadannan bamabaman biranen basu taba samun wani mummunan hari ba a cikin shekaru biyar da aka kwashe ana yakin basasa a kasar..
Bamabamai hudu tare da harin kunar bakin wake suka afkawa birnin Jableh. Hare-haren sun shafi kofar shigar gaggawa ta asibitin birnin. Wata roka kuma da aka jefa ta fada kan motar safa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane hamsin da uku.
Wasu bamabamai uku da suka hada da kunar bakin wake kuma sun farma garin Tartus mai tazarar kilomita sittin daga garin Jableh lamarin da shugaban Syrian Observatory, Rami Abdel Rahman yace ba'a bata ganin irinsa ba.
Baicin hakan 'yan ta'adan sun auna hari akan wata motar safa kamar yadda kamfanin yada labaran Syria wato SANA ya shaida. Gidan talibijan din kasar yace akalla dan kunar bakin wake daya ya tarwatsa kansa kusa da tashar mota kana jim kadan wani kuma ya biyo shi da mota shake da bamabamai. A nan mutane arba'in da takwas suka rasa rayukansu.
Wata kafar yada labaru dake da alaka da kungiyar ISIS tace kungiyar ce ta kai hare-haren