Kungiyar Taliban ta Afghanistan ta fadi cewa an nada Mawlawi Haibatullah Akhunzada a matsayin sabon shugaban kungiyar biyo bayan mutuwar Mullah Akhtar Mansoor.
A wata sanarwa da suka fidda yau Laraba da harshen Pashto, ‘yan kungiyar ta Taliban sun kuma tabbatar da cewa an kashe Mansoor a wani harin jirgin sama mara matuki da Amurka ta kai cikin makon da ya shige.
A shekaranjiya Litinin, Shugaban Amurka Barak Obama ya tabbatar da cewa an kashe Masoor, saboda yana hana samun nasara a kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya a Afghanistan.
Sabon shugaban na kungiyar Taliban a Da shine mataimakin Mansoor tare da Sirajuddin Haqqani, shugaban ‘yan Haqqani.
Sai dai har yanzu Haqqani na nan rike da mukaminsa yayinda aka nada dan wanda ya fito da kungiyar, Mulla Yaqoob a matsayin mataimaki na biyu ga shugaban kungiyar.
Sanarwar ta yau Laraba ta fito ne bayan da wani dan kunar bakin wake na kungiyar Taliban ya kashe akalla mutane 11 tare da raunata wasu da dama a Kabul. ‘Yan sandan Afghanistan sun ce harin ya auna wata mota ne dauke da jami’an ma’aikatar shari’a.