An kama mayakin da ake zargi da kitsa harin kunar bakin wake a wajen tashar jiragen saman birnin Kabul yayin rudanin janyewar sojin Amurka a 2021, kamar yadda Shugaba Donald Trump ya bayyana a jiya Talata.
Maharin ya tada bam din da ke jikinsa a tsakiyar taron mutanen da ke neman arcewa daga Afghanistan, inda ya hallaka 'yan kasar 170 da sojin Amurka 13 da ke tsaron kewayen wurin, kwanaki bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko da babban birnin kasar.
A jiya Talata, a jawabinsa na farko ga Majalisar Dokokin Amurka tun bayan komawarsa fadar White House a wa'adi mulkinsa na 2, Trump ya sanar da cewa kasar Pakistan ta taimaka wajen kama rikakken dan ta'addan da ke da hannun wajen aikata danyen aikin."
"Kuma a halin yanzu yana kan hanyarsa ta zuwa Amurka domin fuskantar tsarin shari'armu da baya bata lokaci," a cewarsa.
Ya kuma godewa Pakistan "da ta taimaka wajen kama wannan dodon" sai dai bai yi karin haske game da mutumin ko yadda aka kama shi ba.
A ranar 31 ga watan Disamban 2021, Amurka ta janye ragowar dakarunta daga Afghanistan, inda ta dakatar da rudanin debe dubun dubatar mutanen kasar da suka yiwa tashar jiragen saman birnin Kabul tsinke da nufin hawa jirgin da zai fitar dasu daga kasar.
Dandalin Mu Tattauna