WASHINGTON, DC —
Kerry yace za’a ci gaba da kokarin neman hanyar sulhunta tarzomar kasar duk kuwa da wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka da Rasha din suka kulla.
Tun ranar Litinin dai Amurka da Rasha suka cimma matsayar cewa zasu tsinke tattaunawar da suke ta neman tsaida yakin da ake gwabzawa a Syria, bayan da Amurka ta zargi Rasha da laifin kin cika nata sharudda na yarjejeniyar, musamman wanda ya shafi tsaida fadan da kuma taimakawa wajen bude hanyoyin shiga da kayan agaji don tallafawa wadanda rikicin ya rutsa da su.
A nata gefen, Rasha ta bayyana jin takaici da wannan matakin da Amurka ta dauka, inda ita ma ta zargi Amurka da cewa ta kasa banbantawa tsakanin mayakan ‘yan tawaye da na ‘yan jihadi.