WASHINGTON, DC —
Daga cikin jimillar ‘yansanda 12,801 da aka dakatar, harda manyan hafsoshi ko shugabannin ‘yansanda kamar 2,500, a cewar wata sanarwar gwamnati da aka fitar.
An dai bada sanarwar dakatarda wadanan ‘yansandan ne kwana daya bayanda gwamnatin Turkiyya ta bada sanarwar cewa zata tsawaita dokar ta-bacin da ta kafa da tsawon karin wattani ukku masu zuwa nan gaba. Wannan dokar-ta-bacin da aka kafa jim kadan bayan yunkurin juyin mulkin da aka kafa dai ta baiwa gwamnati damar kama ma’aikatan gwamnati da yawa da ake zargi da cewa suna da hannu a yunkurin.
Daga lokacinda aka yi yunkurin zuwa yau, an kori ma’aiatan tsaro da suka hada da soja, ‘yansanda da na hukumomin shara;a sunfi dubu 100, an kuma kama mutane sun haya dubu 30 da laifin taka rawa a yunkurin.