WASHINGTON, DC —
Yan Gudun Hijiran Afghanistan Fiye Da Dubu 200 Suka Koma Kasarsu

Majalisar Dinkin Duniya tace ‘yan gudun hijiran kasar Afghanistan su fiye da dubu 200 ne suka koma kasarsu daga Pakistan, fiye da rabinsu a cikin makkonin nan, duk da ganin yadda mayakan Taliban ke kara tsananta hare-haren da suke kaiwa a cikin Afghanistan din.