Karawar da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Repblican Mike Pence da Tim Kiane na Democrat yana zuwa ne kwanaki kacal, kamin Donald Trump da Hillary Clinton su kara a karo na biyu.
Jiya Litinin ‘yan takarar guda biyu sun ci gaba da sukar juna, inda Ms. Clinton ta caccaki Trump akan batun haraji shi kuma Trump ya caccake ta akan batun yin amfani da adireshin email wanda ba na gwamnati ba yayinda take sakatariyar harkokin wajen Amurka.
A wani gangami da tayi a jihar Ohio wacce take da matukar tasiri a zaben nan, Clinton ta fadi cewa Trump ya fito ne daga “irin tsarin nan da baya mutunta mai karamin karfi, kuma zai kara karfafa shi muddin ya zama shugaban kasa.”
Ms. Clinton ta danganta sabon zarginta akan Trump biyo bayan rahoton jaridar NEW York Times wanda ya nuna harajin dan takarar na jam’iyyar Republican na shekarar aluf dari tara da cisi’in da biyar inda ya bayyana cewa yayi hasarar dala miliyan 916 daga sana’arsa ta caca da kuma wasu sana’o’in. irin wannan adadin ka iya sa attajirin mai sana’ar saida gidaje ya kaucewa biyan haraji har na tsawon shekaru 18 a hukumance.