Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ai A Kudancin Sudan Sun Ce Mutane Kimanin 200 Ne Suka Mutu A Farmakin Makon Jiya


Shugaban Kudancin Sudan, Salva Kiir Mayardit
Shugaban Kudancin Sudan, Salva Kiir Mayardit

Wannan adadi ya ninka na farko da aka bayar tun lokaci da sojoji masu biyayya ga George Athor suka kai farmaki a Jihar Jonglei

Jami’ai a yankin Kudancin Sudan sun ce harin da wasu sojojin tawaye suka kai a makon jiya cikin yankin ya kashe mutane kimanin 200, abinda ya ninka adadin da aka bayar tun da farko.

Sakatare janar na jam’iyyar SPLM mai mulkin Kudancin Sudan, Pagan Amun, ya fada yau talata cewa an kashe mutane 197 a wadannan hare-hare a gundumar Fangak dake Jihar Jonglei. Wani jami’in dabam, James Kok, wanda shine minista mai kula da ayyukan jinkai, yace mutanen da suka mutu guda 211 ne.

Dukkan jami’an biyu sun ce akasarin wadanda aka kashe fararen hula ne.

A ranakun laraba da alhamis da suka shige mayaka masu yin biyayya ga wani bijirarren hafsan soja, George Athor, sun kai hare-hare a Jihar Jonglei. Athor ya kaddamar da tawayensa ne a bayan da aka kayar da shi a zaben gwamnan Jihar Jonglei a watan Afrilun bara. Kungiyarsa ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a watan janairu, ‘yan kwanaki kadan kafin yankin na kudancin Sudan ya jefa kuri’a mai tarihi ta ballewa daga sauran Sudan.

A baya, rundunar sojojin kudancin Sudan ta ce mutane 105 ne suka mutu a wannan tashin hankali cikinsu har da mayakan Athor guda 30.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwa game da fadan na makon jiya, ya kuma yi kira ga dukkan sassan na kudancin Sudan da su gaggauta tsagaita wuta.

XS
SM
MD
LG