Shugaban Sudan Omar al-Bashir, ya fada yau litinin cewa hukumomi a birnin Khartoum zasu yi na'am da sakamakon da yankin kudancin kasar ya gudanar kan 'yancin kai.
Shugaba al-Bashir ya bayyana wannan 'yan sa'o'i kafin a fitar da cikakken sakamakon wannan zabe na raba-gardama da kudancin kasar ya gudanar.
Shugaban ya ce, "yau, zamu fadaqwa duniya aminjcewarmu, tare da mutunta zabin da al'ummar kudu suka yi."
Ya ce kowa ya san da irin zabin da mutanen kudancin Sudan suka yi, domin sun zabi ballewa su kafa kasarsu dabam.
Jami'an zabe a kudancin Sudan sun ce kusan dukkan masu jefa kuri'a sun zabi ballewa daga yankin arewacin kasar a kuri'ar raba-gardama mai tarihi da aka gudanar a watan da ya shige.
An tsara gudanar da wannan kuri'ar raba-gardama a karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta 2005 wadda ta kawo karshen yakin basasa a tsakanin arewaci da kudancin Sudan.
Har yanzu dai akwai sauran batutuwan da bangarorin biyu ba su warware ba, musamman ma makomar yankin Abyei mai arzikin man fetur wanda ke bakin iyakar arewaci da kudancin Sudan.