Shugaban Amurka Barack Obama, yace ya hakikance Masar ba zata koma gidan jiya ba,ganin masu rajin Demokuradiyya sun bayyana burinsu na ganin an kaddamar da zabe sahihi a kusan mako biyunda suka dauka suna zanga zanga kan titunan kasar.
A hira da ya yi da wata tashar talabijin ta Amurka da aka nuna jiya lahadi, shugaba yace Hosni Mubarak ne kadai ya san dan hanzarinda yake bukata kamin ya yi murabus.Yace Amurka ba zata tursasa Mubarak ya bar mulki cikin hanzari ba,duk da haka ya bayyana fatan za’a kafa gwamnatin ‘yan kasa wacce Amurka zata yi aiki da ita a matsayin kawa.
Shugaban na Amurka yace haramtacciyar jam’iyyar Muslim Brtoherhood, jam’iyyar hamayya mafi girma a Masar dake da tsari, daya ce cikin jerin jam’iyun hamayya dake kasar,kuma bata da rinjaye a Masar. Ya yarda cewa wasu daga cikin manufofinta suna bayyana kiyayya ga Amurka.
Shugaba Obama ya yi magana ne a hira da aka nuna kai tsaye da tashar talabijin ta FOX ga Amurkawa a shirye shiryen tashar na nuna kwallon zari ka ruga mai farin jinni a Amurka. An yi wasan ne tsakanin kungiyoyin wasan Green Bay Packers da Pittsburg Steelers.Ana ji kamar mutane milyan dari ne suka kalli wasan.
Shugaban Amurkan yace zai kalli wasan,amma yaki ya bayyana wace kungiya yake goyon baya,domin kungiyar wasan kwallonsa Chicago Bears basu sami kai waga wasan daukan kofin ba.