Sakamakon zaben raba gardamar da aka gudanar na tarihi a kasar Sudan na nuni da cewa, kashi casa'in da tara bisa dari na masu kada kuri’a sun goyi bayan ‘yantar da yankin. Sakamakon da aka buga a yanar gizon hukumar zaben raba gardaman yau lahadi, ya nuna cewa, masu kada kuri’a dubu arba’in da biyar daga cikin miliyan uku da dubu dari takwas ne suka nuna goyon bayan ci gaba da hadin kan yankin da arewaci. Hukumar ta ce sakamakon zaben na wucin gadi ne, sai dai ta bayyana cewa, an kamala kada kuri’a. Ana kyautata zaton fitar da sakamakon zaben na karshe farkon watan gobe na Fabrairu. Kuri’ar raba gardaman na daga cikin yarjejeniyar da aka tsayar cikin shekara ta dubu biyu da biyar da ta kawo karshen yakin basasa da aka yi fama da shi shekara da shekaru a kasar. Jami’an a arewacin Sudan sun ce zasu yi na’am da sakamakon zaben, yayinda ake kyautata zaton kudancin kasar zai ayyana yacin cin gashin kai cikin wannan shekarar. Sai dai har yanzu akwai aiki tukuru gaban bangarorin biyu, da ya kunshi batun iyakoki da ruwaye, da albarkatun mai da kuma makomar yankin Abyei mai arzikin man fetir.
Kashi casa'in da tara bisa dari na masu kada kuri'a a kudancin Sudan suka goyi bayan ballewa.