Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Rasha Sun Kashe Mutum 5 A Gabashin Ukraine


Hare-haren wata shaida ce ga karin wahalar da dakarun Ukraine ke sha a hannun rundunar sojin Rasha wacce ta ninkasu kudi da kayan aiki da kuma yawan dakaru a fadin fagagen daga.

A yau Laraba, kasar Ukraine ta bayyana cewar hare-haren da Rasha ta kaiwa garuruwan dake kusa da filin daga a gabashin kasar sun hallaka akalla mutane 5 tare da raunata wasu 8 ‘yan sa’o’i bayan wani mummunana harin jirgi maras matuki kusa da birnin Kyiv.

Gagarumin ruwan wutar da jiragen saman Rasha marasa matuka suka kai cikin dare sun hallaka mutane 2 a kusa da birnin Kyiv, ciki harda wani ‘yar jaridar Ukraine, kamar yadda kafar yada labaran da take yiwa aiki ta bayyana.

‘Yan jaridar dake yiwa kamfanin dillancin labarai na Afp aiki a Kyiv sun ji karar fashewa bayan da rundunar sojin saman Ukraine tace Rasha tayi barin wuta da jirage sama marasa matuka 177 masu nau’uka daban-daban kan wuraren data kaiwa hari a fadin kasar.

Dakarun Rasha na kokarin kwace iko da garin Kostyantynivka kuma sun tsananta wajen yin luguden wuta akan sansanonin farar hula dake yankin gabashin Donetsk, wanda fadar Kremlin ke ikrarin cewa wani bangare ne na Rasha.

“An hallaka akalla mutane 5 kana an raunata wasu 8 a hare-haren da ake kaiwa Kostyantynivka,” kamar yadda gwamnan yankin Donetsk Vadim Filashkin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Hare-haren wata shaida ce ga karin wahalar da dakarun Ukraine ke sha a hannun rundunar sojin Rasha wacce ta ninkasu kudi da kayan aiki da kuma yawan dakaru a fadin fagagen daga.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG