Bayan kidaya kashi 99% na kuri'un da aka kada, kafar labaran gwamnatin Turkiyya ta ce sama da kashi 51% ne su ka amince, a yayin da kuma kashi 49% su ka ki amincewa. Daga bisani Shugaban Hukumar Zaben Turkiyya ya tabbatar da sahihancin wadannan alkalumomin sannan ya ce za a fitar da sakamakon a hukumance cikin kwanaki 12 masu zuwa.
Erdowan ya gaya ma magoya bayansa da ke cike da murna a harabar gidansa na Shugaban kasa da ke da birnin Istanbul cewa bangaren masu amincewa sun samu kuri'u wajen miliyan 25, wadanda su ka dara na masu kin amincewa da wajen miliyan 1.3. Ya kuma ce wannan kuri'ar ta kawo karshe katsalandan din da sojoji su ka shafe shekaru gommai su na yi a harkar shugabancin kasar.
"A karo na farko a tarihin wannan janhuriyar, za mu canza tsarin shugabancinmu ta hanyar siyasa mai la'akari da ra'ayin jama'a," a cewarsa a takaitaccen jawabin da ya yi.
Wannan kuri'a ta amincewa ta na nufin kenan tasirin Majalisar Dokokin Turkiyya zai ragu matuka. Za a yi watsi da mukamin Firaminista, kuma Shugaban kasa ne zai rika nada Ministoci kai tsaye kuma shi ne za su rika saurare. Haka zalika shugaban kasar ne zai rika fasalta kasafin kudin kasar.
Facebook Forum